Ci Gaba Da Rike El-Zakzzaky Zai Kawo Matsalar Tsaro-Masanin Tsaro

Sheik El-Zakzaky

Masana Shari'a da kwararru kan tsaro na cigaba da tattauna batun cigaba da tsare jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Sheik Ibrahim El-zazzaky.

Barista El-Zubair Abubakar daya ne daga cikin masu fashin baki kan harkar Shari'a kuma ya ce akwai abun lura. Yace kotu ta riga ta yanke hukunci a kan shai’ar al-Zakzzaky kuma ta umarci gwamnati ta gina masa gida a wani wuri ba cikin Zaria ba kana ta bashi kudi amma gwamnati bata yi hakan ba kuma bata daukaka kara ba a kan wannan hukunci wanda shine kadai abin da yakamata tayi.

Wani masanin harkar tsaro a Najeriya Manjo Yahaya Shinko mai ritaya, ya mana tsokaci a kan a kan tasirin fargabar da wasu ke yi cewa sakin sheikh El-zazzaky zai haifar da barazanar tsaro. Yace sakin al-Zakzzaky ba zai kawo matsalar ba illa kwanciyar hankali.

Manjo Yahay ya kara da cewa tun da al-Zakzzaky shine shugaban wadannan mutane kuma wanda za ke musu magana su yi ko kada su yi, don haka ci gaba da rike shi zai kawo babbar illa. Ya kuma ce irin haka ya faru a baya ne yasa aka kai ga samun kungiyar Boko Haram.

Dama dai gwamnan jihar Kaduna Malam Nasuru Ahmad El-rufai ya taba bayyana laifukan sheikh El-zazzaky kamar rashin yarda da gwamnatin Najeriya da kuma yin biyayya ga gwamnatin Iran, da kisa da rufe hanyar gwamnati bada izinin ba da horar da yara suna gadinsa.

Maganar sa tuka-sa-katsi kan shari'ar Sheik Zazzaky dai na cigaba da jan hankalin al'uma musamman ma dai ganin kotu ta bada belin shi.

Wakilinmu a Kaduna Isah Lawal Ikara, na dauke da karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

FASHIN BAKI A KAN KAMA AL-ZAKZZAKY