China ta yi kiran da a daidaita tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

  • Ibrahim Garba

Harin da jiragen yakin Sudan su ka kai Rubkona a Sudan ta Kudu kenan

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce take-taken makwabciyarsu - kasar Sudan - tamkar shelar kaddamar da yaki ne.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce take-taken makwabciyarsu - kasar Sudan - tamkar shelar kaddamar da yaki ne.

Wannan kalamin nasa na yau Talata ya yi ne a yayin tattaunawarsa da Shugaban China Hu Jintao a birnin Beijing. Mr. Kiir ya kai ziyarar kwanaki 5 ne da za ta hada da bude sabon ofishin jakadancin Sudan ta Kudu.

Amurka da China da sauran manyan kasashen duniya sun yi kira ga Sudan da Sudan ta Kudu da su daina fada su koma kan teburin shawara.

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya fadi jiya Litini cewa yanzu babu wani sauran batun tattaunawa kuma, saboda wai Sudan ta Kudu ba ta fahimtar wani bayani idan ba na karfin bindiga da harsashi ba.

Jami’an gwamnatin Sudan ta Kudu sun ce jiragen yakin Sudan sun yi ruwan bama-bamai da daren jiya a Panakwach.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi tir da jefa bama-baman da Sudan ke yi, ya yi kira ga hukumomi a birnin Khartoun su kawo karshen dukkannin tashe-tashen hankula ba tare da bata lokaci ba.

Amurka ma ta yi Allah wadai da abin da ta kira kutsen dakarun Sudan. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Victoria Nuland ta ce Amurka ta yadda cewa Sudan ta Kudu na da ‘yancin kare kanta, to amman ta na kira ga hukumomi a Juba da su kai zuciya nesa wajen mayar da martanin bama-baman da ake masu.