Shugaba Omar al-Bashir na Sudan yace babu sauran tattaunawa da Sudan ta Kudu, a yayin da shaidu a Kudu suke fadin cewa jiragen saman yaki na Sudan sun kai hare-haren bam.
Shugaba Bashir ya bayyana wannan ga sojojinsa jiya litinin a lokacin da ya ziyarci Heglig inda ake hakar mai, wanda kuma sojojin Sudan suka kwato daga hannun sojojin Sudan ta Kudu a ranar jumma'a.
Shugaba Bashir yace babu abinda Sudan ta Kudu ta fahimta im ban da bindigogi da harsasai.
Jami'an gwamnati da kuma shaidu a Sudan ta Kudu sun ce jiragen saman yaki na Sudan sun kai hari cikin Jihar Unity a Sudan ta Kudu jiya litinin, suka kashe mutane uku, ciki har da wani saurayi. An jefa bama-baman ne a ciki da kuma kewayen garin Bentiu dake bakin iyaka.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, yayi tur da hare-haren bam din da Sudan ta kai, ya kuma yi kira ga gwamnati a Khartoum da ta kawo karshen wannan farmaki nan take.