Shugaba Umar Al Bashir ta Sudan yace kasarsa ba zata ci gaba da tattaunawa da Sudan ta kudu ba. Wannan furuci bijirewa kiraye kirayen da kasashen duniya ke yi ne, cewa kasashen biyu su magance sabanin dake tsakaninsu ta hanyarwa tattaunawa.
Yau litinin shugaba Al Bashir yayi wannan furuci a lokacin daya kai ziyarar Heglig mai arzikin mai, yankin da sojojin Sudan suka kwace daga hannun sojoji Sudan ta kudu a ranar juma’a.
A hali da ake ciki, shedun gani da ido da mukadashin hukumar leken asirin rundunar sojan Sudan ta kudu Mac Paul sunce, a yau litinin jiragen saman yakin Sudan suka kaddamar da hare hare a wani yankin kan iyakar Sudan ta kudu harma suka kashe akalla mutum guda.
Jami’in na Sudan ta kudu, Mac Paul ya baiyana hare haren da aka kai Benitiu a zaman tsokana fada kiri kiri. ‘Yan jaridar da suke wurin sun bada rahoton cewa harin ya kashe wani yaro a wata kasuwa.
An kai wannan harin ne kwana daya, bayan da Sudan ta kudu ta kamalla janye sojojinta daga garin Heglig mai arzikin mai, inda sojojin suka mamaye a ranar goma ga watan Afrilu.
Kasashen duniya suna ta matsawa dukkan kasashen biyu lambar, su kawo karshen hare haren da suke kaiwa juna, kuma su sake tada injin din yin shawarwari a tsakaninsu.