A yau Talata kasar China ta maida martani da kakkausan lafazi akan yadda shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da kalmar “kwayar cutar 'yan China” da nufin cutar Coronavirus wadda ta yadu a sama da kasashe 150 a fadin duniya.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Geng Shuang, ya ce, kalaman Trump tamkar nuna kyama ne ga kasar China.
A jiya Litinin, Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Amurka zata tallafa wa kamfanoni kamar na jiragen sama da ma wasu, musamman wadanda kwayar cutar 'yan China ta shafa.
A makon jiya ma Trump ya sanya sakon da wani mutum ya tura a shafin twitter sa, a sakon mutumin, ya bayyana cutar Coronavirus a matsayin “kwayar Cutar China.”
Da aka tambaye shi a wani zaman majalisar dokoki, akan ko ya yake ganin rashin cancantar shugaban kasa yayi amfani da wadannan kalmomin, daraktan cibiyar kare yaduwar cututtuka na Amurka wato CDC, Robert Redfield ya amsa da "Eh" bai dace ba.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanya wa sabuwar cutar ta Coronavirus suna COVID-19.