Sabbin ka'idojin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya ma Amurka game da cutar coronavirus sun hada da abubuwan da ya kamata mutane su yi da wadanda bai kamata su yi ba na tsawon kwanaki 15 daga yanzu.
Ya yi kira ga mutane da su daina cudanya barkatai don a dakile bazuwar wannan cutar.
Da yake bayyana sabbin matakan tare da tawagarsa ta yaki da cutar, shugaban kasar ya fada cewa, mutane su guje zuwa duk wasu taruka na mutane fiye da 10, su kuma gujewa cin abinci a gidajen abinci, da wuraren shaye-shaye da kuma duk wasu tafiye-tafiyen da basu zama tilas ba.
Matakan sun shawarci gwamnoni da su rufe duk wasu wurare da mutane ke haduwa, ciki har da gidajen abinci da wurin motsa jiki da sauransu.
Matakan dai sun bukaci mutane su yi aiki ko karatu daga gida, duk lokacin da hakan zai iya yiwuwa, kuma a guji ziyartar gidajen da ake ajiye tsofaffi ko marasa lafiya.
An karfafa wa gwamnoni gwiwa wajen rufe makarantu da duk wasu yankuna da ake da shaidar an samu yaduwar cutar.
Facebook Forum