A yau Litinin China ta ce za ta yi karin kudaden haraji akan kayayyakin Amurka da ake shiga da su kasarta, wadanda kudinsu ya kai dalar Amurka Biliyan-Sittin.
Wannan mataki da Chinan ta dauka, martani ne kan karin kudaden haraji da Shugaba Donald Trump ya yi akan kayayyakin China da ake shiga da su Amurka, wadanda kudadensu ya kai dalar Amurka Biliyan-dari-biyu.
Ministan kudin kasar ta China, ya ce daga ranar Daya ga watan Yuni, sabon tsarin karin kudaden harajin zai fara aiki, daga kashi biyar zuwa 25, yana mai cewa, karin zai shafi kayayyakin Amurka dubu 5,140, wadanda ake shiga da su Chinan.
Hukumomin Beijing sun kara da cewa, daukan wannan mataki, martani ne kan irin yadda Amurka ke “yin gaban kanta da kuma kara kudaden haraji akan kamfanonin kasashen waje, wadanda ke gogayya da nata.”
A cewar, Ministan, China ba za ta taba mika-wuya ga matsin lambar wata kasar waje ba, “domin China tana da karfin da za ta kare kanta da hakkokinta, amma muna fatan za mu samu daidaito da Amurka a nan gaba.”