A ranar Juma'a Juma’a China ta gargadi Japan kan cewa "ta kuka da kan ta" idan har ta yi katsalandan ga shirin da Beijing take da shi game da Taiwan, tsibirin mai cin gashin kansa, wanda Beijing din ta dauka a matsayin lardin ta da ya balle, wanda kuma dole ne wata rana ya sake hadewa da babban yankin, ko da kuwa ta karfin tuwo ne idan ta kama.
Ofishin jakadancin China da ke Tokyo ne ya ba da wannan gargadin bayan wata ziyara da wasu gungun ‘yan majalisar dokokin Japan suka kai a kasar Taiwan a wannan makon, ciki har da tsohon ministan tsaro Shigeru Ishiba, dan takarar da ake hasashen zai iya zama Prime ministan kasar na gaba.
Ishiba, dan jam'iyyar Liberal Democratic Party, ya ce shugaban kasar Taiwan Lai Ching-te da Japan suna da ra’ayi daya na wanzar da zaman lafiya a mashigin Taiwan ta hanyar kara tsayin daka da turjiya kan ta'addancin kasar China.
Ishiba ya yi wannan tsokaci ne a wani taron manema labarai a ranar Laraba a ma'aikatar harkokin wajen Taiwan a karshen ziyarar 'yan majalisar.
Bayan ganawarsa da Lai a ranar Talata, Ishiba ya shaidawa manema labarai cewa, bangarorin biyu sun tattauna sosai kan kaucewa rikici da China, wadda wasu ke fargabar tana iya mamaye Taiwan kamar yadda Rasha ta yi wa Ukraine.
Tsohon ministan tsaron ya ki fadawa manema labarai yadda Japan za ta mai da martani idan yaki ya barke a mashigin Taiwan.