Kasar China ta haramta gudanar da duk wata sabuwar huldar kasuwanci da Korea ta Arewa, kamar yadda ma’aikatar hadahadar kasuwancin kasar ta fada a wata sanarwa.
Wannan mataki da Chinan ta dauka, na daga cikin matsayar da aka cimma a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a farkon watannan.
An wallafa sanarwar ne shafinta na yanar gizon ma’aikatar, inda aka nuna cewa, wannan mataki zai fara aiki ne nan take, inda ta jaddada cewa duk wata sabuwar hulda da ta shafi mallaka ko fadada harkokin kasuwanci da wani mutum ko kamfani daga Korea ta Arewa a China, ta zama haramtacciya.
Ma’aikatar har ila yau ta bayyana cewa, ba za ta rattabu hanu akan wata sabuwar hulda kasuwanci da ‘yan China ke so su kafa ko wata masana’anta a Korea ta Arewa ba.
A farkon watannan nan ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da sabbin takunkumi akan Korea ta Arewa, bayan da ta yi gwajin wasu makamai masu linzami kirar ballistic, da za a iya harbawa daga wata nahiya zuwa wata, da zimmar kwance mata damarar yaki.