WASHINGTON, DC —
Har yanzu dai, tana kasa tana dabo a kan ko wace kungiya ce zata zamo zakarar wasannin lig-lig na firimiya na Ingila bana, a yayin da aski ya zamo gaban goshi.
A jiya lahadi, kungiyar Chelsea, wadda take ta biyu a saman teburin, ta doke Liverpool, wadda take ta daya, kuma sanadinsa shi ne kuskuren da kyaftin na Liverpool, Steven Gerrard yayi aka jefa kwallon farko dab da tafiya hutun rabin lokaci. Amma wadda ta ci gajiyar wannan nasara da Chelsea ta samu a kan Liverpool, ita ce Manchester City.
A sakamakon wannan wasa dai, yanzu ratar da Liverpool ta ba Chelsea ya komo maki biyu kawai. Har yanzu Manchester City tana ta uku, amma tana da karin wasa guda fiye da sauran kungiyoyi biyu dake gabanta, kuma maki uku rak ya raba ta da Liverpool dake sama.
Ma’ana, idan har ta lashe sauranw asannin nata guda uku, ita ce zata zamo zakarar Firimiya Lig ta bana a Ingila, ko da Chelsea da Liverpool zasu lashe sauran wasanninsu. Karin dalili na wannan shi ne City ta jefa kwallaye fiye da sauran kungiyoyin biyu, don haka ko da zasu karasa da maki daidai wa daida, City ce zata zamo zakara a saboda yawan kwallayenta.