Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, dake kasar Ingila, ta cimma yarjejeniya tsakaninta da takwararta ta Atletico Madrid, kan batun sayar da dan wasan gabanta Diego Costa.
Duk da wannan yarjejeniyar da Kungiyoyin biyu suka yi dan wasan ba zai buga wa Atletico wasa ba sai watan janairu na shekara ta dubu biyu da goma sha takwas a lokacin an daga wa kungiyar ta Atletico Madrid takumkumin sayen 'yan wasa da aka kakaba mata sakamakon karya daukar cinikin 'yan wasa da tayi a shekarun baya.
Diego Costa, wanda har yanzu bai takawa kungiyar sa ta Chelsea leda a wannan kakar wasanin ko sau daya ba, ya share dogon lokaci yana zaune a kasarsa ta haihuwa Brazil.
Dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa ya zo kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ne a shekara ta 2014 akan kudi fam miliyan £32 daga kungiyar ta Atletico Madrid.
Diego, ya buga wasanni 120 a kungiyar ta Chelsea, ya samu nasarar jefa kwallaye 58, cikin su harda kwallaye 20 a gasar Firimiyar da ta gabata ta 2016/17 na kasar Ingila.
A tun bayan kammala wasannin shekara ta 2016/17 Diego Costa ya nuna sha'awarsa ta Komawa tsohuwar Kungiyarsa ta Atletico Madrid, inda yace sam baya jin dadin zama a kungiyar Chelsea, sakamakon wulakancin da yace ana masa.
Ita kuma kungiyar ta Chelsea tuni ta maye gurbin sa da dan wasan gaba na Real Madrid, Alvaro Morata, a farkon kakan wasan bana.
Your browser doesn’t support HTML5