A cigaba da wasannin da akeyi na kwallon kafa a bangaren gasar cin kofin English football league, na kasar Ingila. Jiya an fafata wasannin goma sha daya, inda kungiyar kwallon kafa ta Leicester city, tayi waje rod da takwararta ta Liverpool, da kwallaye, 2-0.
Dan wasan gaba na Leicester Cty, mai suna Shinji Okazaki, shi ya jefa kwallon farko a ragar Liverpool, a minti na 66 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, daga bisani ana minti na 78, sai Islam Slimani, na Leicester, ya kara kwallo ta biyu haka dai aka tashi a wasan. 2-0.
Wannan nasara da Leicester ta samu ya bata damar zuwa wasan zagaye na gaba, a gasar, a tarihin haduwar kungiyoyin biyu tun bayan kafuwarsu, wannan shine karo na ashirin da hudu da kungiyoyin ke haduwa.
Sai dai ita kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, tayi nasara akan Leicester city, sau goma sha daya, Ita kuwa Leicester ta samu nasarar doke Liverpool ne sau takwas inda akayi kunnen doki sau biyar.
A sauran wasannin da aka buga a jiya na EFL Crystal palace 1-0, Huddersfield Town,
Bristol City 2-0 Stoke City, Burnley 2(3-5)2 Leeds United, AFC Bournemouth 1-0 Brighton & Hove, Wolverhampton 1-0 Bristol Rovers, Westham 3-0 Bolton Wanderers,
Aston Villa 0-2 Middlesbrough's, Brenfortd 1-3 Norwich city Tottenham 1-0 Barnsley,
A yau kuma za'a cigaba da karawa a sauran wasannin inda kungiyar kwallon kafa ta Chelsea zata kara da Nottingham Forest, sai Arsenal da Doncaster Rovers, Everton da Sunderland.
Sai kuma Manchester United ta karbi bakuncin Burton Albion, ita kuwa Westbromwich su fafata da Manchester City, za'a fara wasanne tun daga misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, Kamaru, da kasar Chadi.
Facebook Forum