A yau litinin 18 ga watan Satumba shekara dubu biyu da sha bakwai, (2017) Wata koto a kasar Ingila, ta yanke wa tsohon jagoran ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Ingila, wanda yanzu yake taka leda a kungiyar Everton, Wayne Rooney, hukuncin hanashi tuka mota a kasar Ingila, har na tsawon shekaru biyu, bisa samun shi da laifin tuki cikin maye.
Dan Sanda mai gabatar da karar yace a farkon wannan watan na Satumba 2017 da muke ciki ne hukumar ‘yan Sandan bangaren Cheshire, dake kasar ta Ingila, ta kama dan wasan da yin tuki cikin maye, da ya wuce ka’ ida akan hanyar Altrincham,
A bisa dokar kasar Ingila tuka mota cikin maye ya saba wa dokar tukin kasar. Bayan amsa laifinsa da kuma dakatar dashi daga duka mota na tsdawon shekareu biyu, har ila yau koton ta ci tarar Rooney, kudi fam dari da saba'in.
Wayne Rooney, mai shekaru 31, da haihuwa yayi nadaman aika wannan laifin, ya kuma yi na'am da hukunci da kotun ta yanke masa.
Daga karshe ya neme afuwa daga yan'uwa da kuma manajansa, da shuwagabanin kungiyar Everton, tare da dukkan magoya bayansa, a duniya, bisa wannan abun da ya aikata, yana mai cewa dole ne abun ya bata musu rai ganin irin kwaunar da suke masa.
Facebook Forum