Cefanen 'Yan Wasan Da Muka Yi Ya Sa Mun Fara Ganin Gabanmu  – Solskjaer

Ole Gunnar Solskjaer

Ole Gunnar Solskjaer ya kuma yi fatan idan Manchester United ta lashe kofuna, hakan zai ba Paul Pogba kwarin gwiwar ci gaba da zama a kulob din.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer, ya ce cefanan ‘yan wasan da kungiyar ta yi ya kara mai kwarin gwiwar cewa farin lashe kofi da kungiyar take fama da shi, ya zo karshe.

United ta sayo manyan ‘yan wasa da suka hada da Raphael Varane, Jadon Sancho da Crsitiano Ronaldo, abin da ya sa Solskjaer ya ce kulob din ta cika burinta a shirin da take yi don tunkarar wannan sabuwar kakar wasa.

Sama da shekara hudu rabon da Manchester United ta daga kofi.

“Mun gaji da yin kasa a gwiwa, ko da yake, mun yi rawar gani a wasu lokuta, amma wannan kulob din ta bunkasa cikin kakar wasannin da suka gabata.”

“Kasancewarmu da ‘yan wasa irinsu David (De Gea) da Harry Maguire da ya dan kwana biyu a nan, hakan ya karawa kulob din kaimi. Sannan ga Raphael Varane da Cristiano Ronaldo da suka zo.” Solskjaer ya ce kamar yadda Sky Sports ya ruwaito.

Ole Gunnar Solskjaer ya kuma yi fatan idan Manchester United ta lashe kofuna, hakan zai ba Paul Pogba kwarin gwiwar ci gaba da zama a kulob din.

A karshen makon da ya gabata, Manchester United ta lallasa Newcastle da ci 4-1 inda Ronaldo ya ci kwallaye biyu.

Wannan shi ne wasan farko da Ronaldo ya bugawa United tun bayan komen da ya yi zuwa kulob din daga Juventus.

A halin yanzu Manchester United ce a saman teburin gasar ta Premier.

Manchester United za ta kara ne da West Ham a wasanta na gaba wanda za a yi a ranar Lahadi.