Ce-Ce-Ku-Cen Masana Kan Hukumar Tsaro Ta Amotekun

Hukumar Tsaro Ta Amotekun

Tun bayan da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana kafa sabuwar hukumar tsaro da gwamnatocin jihohin kudu maso yammacin kasar suka kafa, wanda ake wa lakabi da rundunar "Amotekun," a matsayin haramtacciya, batun ke ci gaba da jawo cece-kuce a tsakanin masu fashin baki da masana.

Muhammad Ismail, wani tsohon Editan Jaridan Leadership, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, na ganin idan aka bi ta barawo to kamata ya yi a bi ta mabi sawu.

Hukumar Tsaro Ta Amotekun

Lauya mai zaman kansa Barr. Idris Abdullahi Jalo na ganin lamarin ne ta fuskar sharia, in da ya ce, kafa wannan hukumar tsaro "Amotekun" ba a yi shi bisa ka’ida da doka ba.

Masana a harkar tsaro kamar ASP Yakubu Sule, wani tsohon jami’in tsaro a Najeriya, ya ce ko a harkar tsaro hukumar tsaron ta Amotekun za ta iya taimaka wa jami’an tsaro.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Cece - Kucen Masana Akan Hukumar Tsaro Ta Amotekun