Hukumomin Najeriya, sun ce kafa rundunar tsaro ta "Amotekun" da jihohin kudu maso yammacin Najeriya suka yi, ya sabawa dokar kasa.
A makon da ya gabata ne gwamnonin Jihohin kudu maso yammacin Najeriya, suka kaddamar da wani shiri na samar da jami’an tsaro mallakar jihohin da ake kira "Amotekun."
Sai dai gwamnatin tarayyar ta ba da sanarwar cewa, hakan ya sabawa kudin tsarin mulkin kasa.
Sanarwar da mai bai wa Ministan Shari’a kuma Atoni Janar Abubakar Malami shawara, Dr. Umar Jibril Gwandu ya sakawa hannu, ta ce matakin ya sabawa doka.
Ana dai ganin cewar gwamnatin tarayya ta gaza wajen samar da tsaro, shi ya sa jihohin suka tashi tsaye wajen samar da jami’an tsaro mallakarsu.
“Babu wata doka da ta bai wa gwamnoni damar kirkirar kowace irin runduna don samar da tsaro, wannan wani aiki ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tarayya." inji Dr. Gwandu, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Muryar Amurka.
Ya kara da cewa, wannan jami’an tsaron ba su da wani hurumin gabatar da aiki.
Ya kuma musanta zargin da ake yi cewa, gwmanati ta gaza wajen samar da tsaro, inda ya kara da cewar “gwamnati na iya kokarinta na ganin ta samar da tsaro, don kuwa babu inda ta gaza a wannan fannin.
Ya zuwa yanzu, babu wani rahoto da ya nuna ko gwamnonin yankin kudu maso yammacin na Najeriya sun mayar da martani kan wannan sanarwa ta hukumomin Najeriya.
Amma kungiyar daliba ta kasa NAN, ta nuna goyon bayanta ga kafa rundunar, tana mai cewa tana taimakawa wajen yaki da masu satar mutane, kamar yadda jaridar Thisday ta ruwaito a wannan mako.
Ga hirarsu cikin sauti.
Facebook Forum