Yanzu haka dai hankulan 'yan jarida a Najeriya na kara tashi sakamakon barazanar da ake yi ga rayukan 'yan jarida a kasar inda ake binsu har gida a sace su ko kuma ma a kashe su.
Na baya nan shi ne kisan da wasu da ba'a gane ko su wane ne ba, suka yi wa wani dan jarida Maxwell Nashon, da ke aiki da gidan radiyon Fombina FM, a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashi.
Kamar yadda 'yan uwa da abokanan aikinsa suka tabbatar, wasu da ba'a san ko su wane ne ba suka bi dan jaridan har gida cikin dare suka fitar da shi zuwa wani waje inda suka sassare shi har ya rasa ransa.
Rahotanni daga Najeriyar na cewa, wasu mata manoma ne suka tsinci Nashon shame-shame cikin jini.
Abdullahi Tukur wakilin gidan radiyon Najeriya FRCN, da ke zama shugaban kungiyar wakilan kafofin yada labarai a jihar Adamawa, wato "Correspondents Chapel" ya ce wannan al'amari ya matukar kada su.
Ya kuma yi kira da a tabbatar an zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Shi dai Nashon ya taba aiki da FRCN.
Rundunan 'yan sandan jihar Adamawa ta bakin kakakinta DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya tabbatar mana da faruwan wannan lamarin da kuma matakin da aka dauka.
Cikin kwanakin nan an samu karuwar cin zarafin 'yan jarida a Najeriya, batun da ke kara ta da hankulan manema labarai.
Ga rahoto cikin sauti daga jihar Adamawa.
Facebook Forum