CBN Ya Amince Da Sakin Kunshin Dokokin Musayar Kudade

Babban bankin Najeriya CBN

A cewar sanarwar da CBN din ya fitar, kunshin dokokkin zai zamo jagora ga bangaren bankuna wajen dabbaka halaye nagari a tsakanin dillalan da aka sahalewa yin hada-hada a kasuwar musayar kudaden Najeriya.

Babban bankin najeriya (CBN) ya bayyana cewar ya amince da sakin dokokin musayar kudade na Najeriya.

CBN ya kuma sanarda cewar za’a kaddamar da kunshin dokokin a mako mai zuwa a Abuja.

A cewar sanarwar da CBN din ya fitar, kunshin dokokkin zai zamo jagora ga bangaren bankuna wajen dabbaka halaye nagari a tsakanin dillalan da aka sahalewa yin hada-hada a kasuwar musayar kudaden Najeriya.

Sanarwar ta kara da cewar, “CBN ya amince a saki kunshin dokokin domin yin jagora ga bangaren bankuna wajen dabbaka halaye nagari a tsakanin dillalan da aka sahalewa yin hada-hada a kasuwar musayar kudaden najeriya.

“Babban bankin zai kaddamar da kunshin dokokin a hukumance a babban dakin taro na shelkwatarsa dake abuja, a ranar talata, 28 ga watan Janairun 2025.