Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Bunkasa A Zango Na 3 Na 2024 - CBN


Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

An samu sassauci a hauhawar farashi a zangon shekarar, inda ya nuna samun ragowa a farashin kayan abinci daga cikin kunshin kayan masarufin da ake bukata,

Tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kaso 3.46 cikin 100 a zango na 3 na 2024, inda yawan abinda aka fitar ya kai Naira tiriliyan 20.115, daga kaso 3.19 cikin 100 (tiriliyan 18.285) da yake a zango na 2 na 2024, inda galibi bangaren da babu ruwansa da man fetur ne ya taka rawa.

Hakan na kunshe ne a sabon rahoton tattalin arzikin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar kan zango na 3 na 2024.

A cewar rahoton, an samu sassauci a hauhawar farashi a zangon shekarar, inda ya nuna samun ragowa a farashin kayan abinci daga cikin kunshin kayan masarufin da ake bukata, inda matakin takaita amfani da tsabar kudi ya taka muhimmiyar rawa.

Yawan danyen man da Najeriya ke hakowa ya karu, sakamakon inganta tsaro a kewayen bututun man da ke yankin Neja Delta.

Duk da matsalolin da suka ci gaba da bijirowa, CBN ya ce tattalin arzikin ya ci gaba da bunkasa a zango na 3 na 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG