Canje Canje da ya Dace da zamani a Muryar Amurka

VOA LOGO

An bukaci wakilan gidan Rediyon muryar Amurka, dasu rungumi sabbin dabarun aikin jarida domin tafiya da zamani.

Malama Debuski, daya daga ciki wadanda suka ja ragamar taron bita da gidan Rediyon muryar Amurka, ya shiryawa wakilansa dake Najeriya, tace makasudin wannan taron shine dan tabbatar da wakilan gidan Rediyon muryar Amurka, na rubuta labarai, kan kiwon lafiya da ilimi, ta hanyar haduwa da mutane da kuma sada su da juna saboda aikin jarida na canjawa da gaggawa a wannan zamani na internet.

Tace akwai bukatar wakilan na muryar Amurka, su tabbatar cewa masu sauraro na fahimtar me ake Magana akai.

Shi kuwa shugaban sashen Hausa na muryar Amurka, Mr. Leo Keyan, ya bayyana irin canje canjen da sashen ke fuskanta domin ya dace da wannan zamani, kuma ya tabbatarwa masu sauraro cewar muryar Amurka, zata cigaba da jan ragama ta cimma bukatun masu sauraro.

Ya kara da cewa kwananan sashen hausa na muryar Amurka zai kaddamar da tashan Talebijin mai suna “VOA Hausa TV.”