CAF Ta Fidda Sunayen 'Yan Wasa 5 Domin Cin Kyautar Gwarzon Dan Wasa Ta Bana

Dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman

A yayin dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman ya samu shiga cikin gwaraza 5 din, jagoran tawagar kasar, William Troost-Ekong bai samu shiga cikin jerin sunayen mutum 9 na farko ba.

A yau Litinin, hukumar kwallon kafar nahiyar Afrika (CAF) ta bayyana sunayen gwarazan 'yan wasa 5 a ajin maza a hukumance domin fafatawa wajen lashe kyautar gwarzon dan wasan caf ta 2024.

A yayin dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman ya samu shiga cikin gwaraza 5 din, jagoran tawagar kasar, William Troost-Ekong bai samu shiga cikin jerin sunayen mutum 9 na farko ba.

An tsara bikin bada kyautar gwarzon caf din ta bana ta gudana a birnin Marrakech, na kasar Morocco a ranar 16 ga watan Disamba mai zuwa.

'Yan wasan da suka samu shiga cikin jerin gwaraza 5 din sun hada da Simon Adingra (dake bugawa kasar Ivory Coast da kungiyar Brighton da Hove Albion wasa) da Serhou Gulrassy (dake bugawa kasar Guinea da kungiyar Borussia Dortmund wasa) da Achraf Hakimi (dake bugawa kasar Morocco da kungiyar PSG wasa) da Ademola Lookman (dake bugawa Najeriya da kungiyar Atalanta wasa) da Ronwen Williams (dake bugawa Afrika ta Kudu da kungiyar Mamelodi Sundowns wasa) dukkaninsu za su fafata domin lashe kyautar gwarzon dan wasan CAF ta bana.

Sauran rukuninin kyautar da aka sanar a yau sun hada da gwarzon mai tsaron raga na bana da dan wasan mafi kwazo fafatawa tsakanin kungiyoyi da gwarzon mai horar da 'yan wasa na bana da dan wasa mafi kakantar shekaru na bana da kuma gwarzuwar tawagar kwallon kafar kasa ta bana.