Burtaniya ta kara tsaurara matakan kariya daga hare-haren ta’addanci, bayan wani harin bam da aka kai a tashar jirgin kasa, wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa.
A jiya Juma’a, Firai Minista Theresa May, ta bayyana daukan wannan mataki, wanda Cibiyar nan ta hadin gwiwa mai bin diddigin hare-haren ta’addanci, ta ba da shawarar a yi – inda aka kai baranzar harin ta’addanci zuwa ma’auni na karshe.
Firai ministar ta kara da cewa, dakarun kasar za su fara taimakawa ‘yan sanda wajen ba da tsaro a wasu wurare, tana mai cewa al’umar kasar za su ga karin jami’an tsaro akan tituna, ba kamar yadda aka saba gani a baya ba.
Yayin da hakan ke faruwa, kungiyar IS, ta ce wani reshenta ne ya dana bam din da aka tayar a tashar Parsons Green Subway, wanda ya raunata mutane 29.
Bam din ya tashi ne, a daidai lokacin da ake samun cunkoson jama’a, a harin wanda ‘yan sanda suka ayyana shi a matsayin na ta’addanci.
Daga cikin wadanda suka jikkata, babu wanda rayuwarsa ke cikin hadari, in ji ma’aikatan ba da agajin gaggawa.