Cikin kakkausan harshe, Korea ta Arewa, ta soki matsayar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka a jiya Talata, na saka mata tsauraran takunkumi, inda har ta yi barazana ga Amurka, kan cewa za ta dandana kudarta, saboda rawar da ta taka wajen cimma wannan matsaya.
A wani zaman kwance damarar yakin kasar da aka yi a Geneve, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi, Jakadan Korea ta arewa a Majalisar, Han Tae Song, ya ce kasarsu ta kuduri aniyar “amfani da wata hanya” wajen cimma burinta, ba tare da ya fayyace abinda yake nufi ba.
Gabanin saka wadannan sabbin takunkumin, Korea ta Arewan, ta ja kunnen Amurka, kan cewa za ta gane kurenta, muddin ta shige gaba wajen saka tsauraran takunkuman.
A jiya Talata shugaban Amurka ya fadawa manema labarai a Fadar White House cewa “wadannan sabbin takunkuman, somin-tabi ne idan aka kwatanta da abinda zai biyo baya a karshe ga kasar ta Korea ta arewa.”
Banda kasar ta Korea ta arewa, kasashe a yankin Asiya sun yi lale marhabin da wannan mataki, sai dai da yawa na nuna shakku kan ko takunkuman za su yi wani tasiri.
Sabbin takunkuman wadanda suka jibincin tattalin arzikin kasar, martani ne ga gwajin abinda ake ganin makamin hydrogen bom ne da kasar ta yi a ranar 3 ga watan Satumba.
Facebook Forum