Wannan yunkuri na zuwa ne daidai lokacin da wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya mai suna HEDA ta gabatar da bincikenta kan tsare-tsare da dokoki da kuma ayyukan cibiyoyin hada-hadar kudade da ma wadanda ba na kudi ba a kasar Burtaniya da Haddadiyar Daular Larabawa.
Mafi yawan ‘yan Najeriya da suka saci kudin gwamnatin kasar su na kaiwa wadannan kasashe don sayan kaddarori ko boye su a bankuna.
Karin bayani akan: Naira, London, Burtaniya, Nigeria, da Najeriya.
Dangane da wannan batu, Farfesa Abdullah Shehu, kwararre a fanni bincike da ya shafi al’amuran halatta kudaden haram a Najeriya ya ce makasudin binciken da aka yi an duba hanyoyi da dokoki a kasashen nan guda biyu wanda idan ka lura ba wurin da ‘yan Najeriya su ke tafiya a duniya kamar Burtaniya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ya ce binciken ya nuna cewa wadannan wurare guda biya su ne manya manyan wurare da ‘yan Najeriya suka cika kai kudaden haram kuma akwai matakan dokokin wanda Najeriya da irin wadannan kasashen suka dauka na dakile irin wadannan miyagun ayyuka wanda har yanzu tsuguno ba ta kare ba akwai abubuwa da yawa da ya kamata kasashen su dauka.
Farfesa Shehu ya ce akwai yarjejeniya da kasashen biyu na hanyoyin da za su yi bincike idan kudaden Najeriya sun je a kwaso su, amma babban matakin da ya kamata a dauka shi ne duk wanda ya yi barna a Najeriya a gurfanar da shi a gaban kotu kuma ayi kokari a ga an kammala shari’ar don a kwace kudade da kadarorin da ya saya.
A hirarsa da VOA, shugaban kungiyar CISLAC kuma Jagora a hukumar Transparency International a Najeriya, Awwal Musa Rafsanjani, ya ce akwai kin bin dokokin yanzu haka da suke a kasar da kuma rashin cikkakun dokokin za su hana satar ko kuma a dawo da kudaden don yiwa talakawa aiki.
Ya ce akwai mutane da suke ganin sun fi karfin doka saboda suna cikin gwamnati mai ci suna cin karansu babu babbaka wannan yana daya daga cikin dalilan da ya sa ba a samun nasara a yakin da fataucin dukiyar kasar zuwa kasashen waje don haka suke kira ga gwamnati ta tashi tsaye ta kawo dokokin da zasu kawo gaskiya da adalci.
Rafsanjani ya ce idan aka bi tsarin irin wadannan kasashen kamar Hadaddiyar Daular Larabawa to za’a kawo gyara wajan samu nasarar kwato irin wadanan kadarori da kuma hana fitar da irin wadannan kadarori.
Shi ma da ya ke tattaunawa da VOA Shugaban kungiyar HEDA Olarewaju Surajo ya bayyana cewa idon duniya na kan Najeriya a matsayin kasar da cin hanci da rashawa ya yi wa katutu.
Sai dai kuma ba haka abin yake ba ganin sai da hanyoyi biyu za’a iya cin nassarar hakan da yanayi mai kyau don haka suka hada gwiwa da kasashen biyu don nemo mafita.
Najeriya na daya daga cikin kasashe biyar a Nahiyar Afirka da suka yi kaurin suna wajen ta’ammali da kudaden haram, kuma a kalla bincike ya nuna cewa an fitar da kudin Amurka dala biliyan dubu 170 cikin shekaru goma, kana kasar na asarar akalla kudin Amurka tsakanin dala biliyan 15 zuwa 18 a kowacce shekara, duk kuwa da ikirarin da gwamnati ke yi na yaki da cin hanci da rashawa da kuma sama da fadi da kudi al’umma.
Kazalika Kungiyar ta yi kari da cewa za ta hada masu ruwa da tsaki daga cikin wadannan kasashe don sake fasalin da suka dace tare da karfafa sauran kasashen da ke fuskantar irin wannan matsala ta hada hadar kudaden haram.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5