Burna Boy Ya Nemi Afuwar Masoyansa

Burna Boy (Facebook/Burna Boy)

Cikin sanarwar, Burna Boy ya dora laifin makarar da ya yi akan masu shirya wasan.

Mawakin Afrobeats Burna Boy ya nemi masoyansa su yafe masa bisa makarar da ya yi na zuwa wani wasa da aka shirya zai yi a Legas da ke kudancin Najeriya.

An tsara Burna Boy zai fara wasansa na sabuwar shekara da misalin karfe 10 na dare, amma bayanai sun yi nuni da cewa sai karfe 3:30 na safiya ya hau dandamalin wasan.

‘Yan kallo sun nuna bacin ransu saboda Burna Boy wanda ya taba lashe lambar yabo ta Grammy bai ba da hakuri ba.

Hakan ya sa jama’a suka hau shafukan sada zumunta suka yi ta caccakar shi.

Sai dai a ranar Litinin Burna Boy a karon farko ya fitar da wata sanarwa inda ya ba masoyansa hakuri.

Cikin sanarwar, Burna Boy ya dora laifin makarar da ya yi akan masu shirya wasan.

“Al'umar jihar Legas, ina kaunarku, ba zan sake yin hakan ba.” Burna Boy, wanda ke yi wa kansa lakabin “African Gaint” ya ce.