WASHINGTON, D. C. - Filin wasan na kungiyar kwallon kafa ta West Ham ne da ke London.
Hukumar da ke kula da filin wasan na London ta sanar da hakan a shafinta na Twitter.
A ranar 3 ga watan nan na Yuni Burna ya yi wasansa na kade-kade a filin wasan, wani bangare na rangadin da yake yi, wanda ya yi wa take da “Burna Boy’s Love, Damini Tour.”
Yayin wasan wanda aka yi a ranar Asabar, Burna Boy ya kayatar da masoyansa da fitattun wakokinsa.
"SOLD OUT wato an sayar da tikiti na filin wasan kaf!! @burnaboy's RECORD-BREAKING concert, yanzu an sayar da shi gaba da ya a hukumunce!
"Wacce babbar nasara ce ga ɗan wasan Afirka na farko da ya taba tsayawa kwarzo tilo a filin wasa na Burtaniya!" Hukumar filin wasan ta ce.
Wasan ya kuma ya hada da wasu manyan mawaka na duniya irin su Stormzy, Popcaan, da Dave & Jhus wadanda suka taya wannan jarumin na Afirka wajen baiwa dubban masoya kade-kade jin dadi a daren.
Magoya bayansa sun rufa mishi baya suna ta rera waka a duk lokacin da Burna Boy ya ke waka, ya yi wakoki sama da 40.
Daga karshe Burna Boy ya ce “Na gode London da Soyayya da kuanar da kuka nuna min da kuma duk wanda ya goyi bayana wajen kafa tarihi!! Sai mun sake haduwa.”
Bayan an kammala wasan wake-waken, an ba Burna Boy lambar yabo da girmamawa.