Burin Shugaban Amurka Shine Kawar Da Nukiliya Daga Zirin Koriya

Shugaban Amurka Donald Trump

Gabanin ganawar shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un shi ne kawar da duk wani shirin nukiliya daga zirin Koriya

Fadar shugaban Amurka ta White House ta bayyana a jiya Litinin cewa babbar manufar tattaunawa da shugaba Donald Trump zai yi da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, itace kawar da duk wani shirin Nukiliya a zirin Koriyar baki daya, sai munga an dau kwakkwarar mataki a kan kawo karshen shirin nukilkiyar kwata kwata, in ba haka ba matsin lamba da takunkumai da Amurka ke yiwa Pyongyang zai ci gaba a kan kasar da ta zama saniyar ware.


Ba zamu mutunta kalaman Koriyawa ta Arewa ba, inji sakatariyar yada labarai ta fadar White House, Sarah Huckabee Sanders, yayin da take amsa tambayar sashen labarun Muryar Amurka a jiya Litinin a kan kalaman Pyongyang na kwanan nan.


Kim ya bada sanarwar dakatar da shirin gwajin makaman nukiliya da kaddamar da makamai masu linzami da suke cin dogon zango.

A hali da ake ciki kuma shugaban Faransa Emmauel Macron yana more ziyarar wuni uku da ya kawo nan Washington, inda aka shirya masa liyafar cin abinci a jiya Litinin a Mount Vernon a Virginia, kana ya gana da wasu masu ziyara da yan yawon bude ido a ginin Lincoln Memorial.


Muhimman batutuwa da suka shafi duniya sune zasu dauke hankali a tattaunawarsa da shugaba Donald Trump a madaukakin ofishinsa na Oval a fadar White House.


Akwai yiwuwar Macron zai yi amfani da tattaunawarsa ta White House ya roki Trump kada ya janye daga yarjejeniyar kasashe shida a kan shirin nukiliyar Iran. Da ci gaba da barin sojojin Amurka a Syria, a dai dai lokacinda sake sabunta yarjejenyar da Iran ta karato.


Iran zata dauki duk wani karin takunkumi a matsayin kashe yarjejeniyar kuma tayi barazanar komawa ga shirinta na nukiliya.


Macron yace yana sane da cewar yarjejeniyar Iran tana da rauni duk da haka bai ga wata yarjejeniya banda wace aka rattabawa hanu.