Bukin Tunawa Da Mazan Jiya Thomas Sankara Bayan Shekaru 31

Yayinda ake cika shekaru 31 da kisan gillar da aka yiwa shugaba Thomas Sankara na kasar Burkina Faso, magoya bayan jam’iyar MPN Kishin Kasa, sun shirya wata mahawarar bainar jama’a domin tunawa da kyauwawan dabi’un mamacin, da ake yiwa kallon wani gwarzo mai akidar kare martabar Afrika a idon Duniya.

Muryar marigayi Thomas Sankara kenan lokacin da yake jawabi a taron shuwagabanin kasashen Afrika karkashin inuwar kungiyar OUA wato AU a yau. Yana mai jan hankulansu akan illar bashin da kasashe masu tasowa ke ciyowa daga bankin duniya, da asusun bayarda lamani wato IMF. Gamsuwa da yadda Thomas Sankara ya dage da ayukan maido da martabar Afrika ya sa a yau ake begensa inji Farfesa Boube Na Maiwa malami a jami’ar Sheik Eeik Anta Diop ta Dakar Senegal.

Jam’iyar MPN Kishin Kasa wace aka kafa a karkashin turba irin ta yaki da miyagun halayen shuwagabani, na daukar Thomas Sankara a matsayin wani gwarzon da matasan yau zasu dauki darusa daga tsarin rayuwarsa, mafarin shirya wannan mahawara akan tarihin marigayin. Ahk. Ibrahim Yakubu shine shugaban wannan jam’iyyar.

Shekaru 31 bayan rasuwar Thomas Sankara, iyalinsa da sauran makusantansa na jiran ganin hukumomin Burkina Faso sun zakulo wadanda suka hallaka shi sai dai har yanzu shiru kake ji, abinda HAjiya Rabi Dadi Gauh tace aiki ne dake jiran matasa.

A ranar 15 ga watan october 1987 ne wasu sojoji a karksahin jagorancin Cap. Balise Compaore suka yiwa Cap. Thomas Sankara kisan gilla a lokacin da suke kokarin kifarda da shi, daga karagar mulkin kasar Burkina Faso da ya shafe shekaru kusan 4 akan mulkin. Juyin mulkin da ake hasashen an tsara shi da nufin murkushe fito na fiton da marigayin ya kaddamar da turawa saboda zarginsu da cin hakkokin Afrika da ‘yayanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Bukin Tunawa Da Mazan Jiya Thomas Sankara Bayan Shekaru 31 2'40"