BUKIN KIRSIMETI:Gwamnatin Tarayya Ta Rage Kudin Sufuri

Matafiya

Gwamnatin Tarayya ta sake rage farashin sufurin dogon zango da kashi 50 cikin 100 ga matafiya masu tafiya daga babban birnin Tarayya Abuja zuwa garuruwa da ke nesa daga.

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin fara aiwatar da sabon tsarin An rangwamen sufuri ga matafiya masu dogo zango jiya Talata, jajibirin Kirsimeti, zuwa ranar 5 ga watan Janairu, 2025.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin watanni 12 da Gwamnatin Tarayya za ta ba da wannan karamcin ga matafiya tsakanin jihohin.

Tuni mambobin kungiyar masu motocin alfarma na Najeriya (ALBON) su ka fara aiwatar da rangwamen kashi 50 cikin 100 a kan hanyoyin da aka kebe na dogon zango a fadin kasar.

wata tashar mota a Lagos

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya Talata ta hannun Shugaban kungiyar na kasa Nonso Ubajaka da da kuma Sakataren kungiyar Frank Nneji, sun bayyana cewa, hakan ya biyo bayan yarjejeniyar hadin gwiwa da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da ALBON.

Masu sufurin sun kuma nuna jin dadinsu ga shugaban kasa Bola Tinubu kan amincewa da rangwamen da a cewarsu zai kawo wa jama’a masu tafiye-tafiyen saukin, kasancewa suna cikin kuncin tsadar farashin kayan masarufi.

Hanyoyin da aka kebance tsakanin jihohin da za a yi rangwamen kudi sun hada da: Abuja zuwa Damaturu, Kano, Maiduguri, Makurdi, da Sokoto.

Tashar mota a Obalende, Lagos.

Wadanda suka tashi daga Abuja zuwa sassan Kudancin kasar kuma za su biya rabin kudin sufuri idan za su je Aba, Benin, Enugu, Owerri, Fatakwal, da Umuahia.

Sanarwar ta ce, akwai kuma rangwamen da za a yi don tashi daga Legas zuwa wurare kamar Aba, Abuja, Asaba, Calabar, Enugu, Umuahia, Uyo, Warri, da Yenagoa.

Ga matafiya da za su tashi daga Legas zuwa yankunan Arewa kamar Gombe, Jos, Kaduna, Kano, Lokoja, Maiduguri, Makurdi, Sokoto, Gusau, Jalingo, da Minna, suma zasu amfana da wannan karamcin na gwamnati.