Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsin Tattalin Arziki Zai Shafi Hada - Hadar Kirsimeti a Najeriya


A yayin shirye-shiryen bikin Kirsimeti na bana, al’ummar krista dake mararin zuwan sa a duk shekara, a wannan shekara bikin yazo musu a wani yanayin da basu taba ganin irinsa ba.

Ana gudanar da bikin Kirsimeti a ranar 25 ga watan Disambar kowacce shekara, inda mabiya addinin kirista ke tunawa da haihuwar Isa Almasihu.

Bikin na Kirsimeti a wannan shekara ya sha banban da sauran shekarun da suka gabata, ganin cewa yadda al’ummar Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, wanda ke matukar tasiri a tafiyar da rayuwar al’umma ta yau da kullum.

‘Ƴan Najeriya dake shirin fara gudanar da bikin na Kirsimeti, sun shaida wa Muryar Amurka cewa, matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar, yayi matukar tasiri a shirye-shiryen bikin na bana.

A hirarsa da Muryar Amurka, Pastor Joshua Maikudi Matazu, ya ce duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki, kamata yayi al’ummar Kirista su mayar da hankali wajen ibada a wannan rana, ba wai shagulgula ko kuma kashe kudade babu lissafi ba.

Pasto, Matazu ya kara da cewa, al’ummar Kirista su dukufa da ibada kamar yadda addinin kirista ya koyar, ta haka ne za’a kawo karshen halin kunci da ake fama da shi a kasar.

A daya bangaren, tashin goron zabbi da farashin sufurin motoci yayi a kasar, ya jefa ‘yan kasar cikin wani yanayi, musamman a lokacin na shirye-shiryen gudanar da bikin Kirsimeti, hakan yasa wakiliyar muryar Amurka ta tuntubi Bulama Kaku Ali, dake matsayin shugaban kungiyar NURTW reshen Jihar Yobe, inda ya shaida cewa, hauhawar farashin litar man fetur da ake fama dashi a kasar da kuma kayayyakin da motoci ke bukata kafin yin sufuri, na daga cikin dalilan da yasa farashin kudin sufurin ke ci gaba da hauhawa.

Yanzu dai abin jira gani shine yadda saukar farashin litar Man Fetur zayyi tasiri wajen saukaka lamura a kasar.

Saurari cikakken rohoton:

Matsin Tattalin Arziki Zai Shafi Hada - Hadar Kirsimeti
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG