Bukar Abba wanda ya yi fama da jinya tsawon watanni, ya rasu ne a yayin da ya ke jinya a kasar Saudiyya.
An riga an yanke matsayar yi masa jana'iza a Saudiyya, inda tuni aka fara karbar ta'aziyya a Damaturu babban birnin jihar Yobe.
Bukar Abba na daga cikin shahararrun 'yan siyasa daga arewa maso gabashin Najeriya kuma mai fada a ji a siyasar jihar Yobe, sannan kuma madugu a cikin 'yan siyasa da ke mulki a jihar Yobe.
A shekarar 2019, marigayin ya jingine takarar Sanatan Yobe ta gabas ya bar wa tsohon gwamnan jihar Ibrahim Geidam kujerar, inda ya ce shi ya zama "kakan siyasar jihar Yobe," nan ta ke ya daga hannun Geidam da kuma gwamna Mai Mala Buni don zama Sanata inda Buni ya zama gwamna, matakin da Ibrahim Geidam ya yaba da shi a matsayi dattaku.
Da aka tambayi marigayi Bukar a lokacin ko ya yi ritaya daga siyasa ne gaba daya? Marigayin ya ce sai dai wani matsayi in ya samu a gwamnatin tarayya.
Adamu Burah Potiskum, na daga cikin matasan 'yan siyasa da ke gidan Bukar, ya ce marigayin ya yi kyakkyawan karshe.
Jama'a da yawa sun shaidi marigayi Bukar da fadar ainihin abun da ke zuciyarsa, ko da kuwa hakan zai iya jawo masa suka.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5