Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai sanya hannu kan dokar bai wa matasa dama domin yin takarar shugabanci. Ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na cika shekara uku akan karagar mulki wanda kuma yayi daidai da shekaru 19 da kafuwar dimokradiyya tun shekarar 1999 kawo yanzu.
Yayi amfani da jawaban sa wajen nuna nasarori da gwamnatin sa ta samu ta fuskar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, yaki da cin hanci da rashawa da kuma matakan da aka dauka wanda suka fara samun nasara kamar yadda yace akan yaki da ta’addanci musamman kungiyar nan ta boko haram.
Yayi wannan bayanin ne a daidai lokacin da ‘yan adawa ke sukar lamirin gwamnatin sa ta hanyar tattalin arziki da kuma bazuwar da aka samu na ta’addanci a wasu bangarori da suka wuce na kungiyar boko haram. Wato a yankin Zamfara, Kaduna Benue da Taraba inda yan ta’adda da masu sace sacen mutane da ‘yan fashi da makami suke ci Karen su babu babbaka.
Ya kara da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zasu ci gaba da daukan mataki kuma baza su daga kafa ba sai dukkan mutane da masu daure musu gindi an gurfanar dasu a gaban shari’a. Gwamnatin sa kuma na ci gaba da karfafa jami’an tsaron ta ta hanyar kara musu kayan aiki da kuma kara daukar dakarun da zasuyi aikin tsaro a kasar.
Saurari jawabin da wakilinmu Umar Faruk Musa ya aiko daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5