Buhari Ya Yi Wa Chadi Jaje

Shugaba Idris Deby na Chadi, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyya ga al’ummar kasar Chadi game da tagwayen hare - haren bam din kunar baki a garin N’djamena.

Harin ya hallaka mutane 23 da raunata sama da 100, sannan ‘yan sandan kasar Chadin sun dora alhakin harin a kan ‘yan ta’addar boko haram.

Muhammadu Buhari ya bawa Chadi tabbacin goyon baya musamman in aka yi la’akari da yadda Chadin ke daya daga cikin dakarun neman murkushe ‘yan ta’addar na Boko Haram.

Sanarwar da Daraktan Yada labaran shugaban kasar Garba Shehu ya saka wa hannu tace Buharin ya bugawa shugaban na Chadi Idriss Deby waya ne.

Haka kuma Shugaban ya jajantawa gwamnati al’ummar jihar Bornon Najeriya game da fashewar wasu yasassun ababen fashewa a Monguno, wanda ya hallaka sama da mutane 60.

A karshe Buharin ya tabbatar da cewa dakile ‘yan boko haram shine a sahun gaba a gwamnatinsa.