A kokarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ke yi na ganin an fuskanci alkibilar yaki da cin hanci da karbar rashawa gadan-gadan, gwamnati na daukar mataki kan zargin da ake wa shugabannin kwamitocin da ke yaki da cin hanci da rashawa.
Kwanannan Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bada umarnin rushe kwamitin binciken cin hanci da rashawa da kwato dukiyoyi da kaddarorin gwamnati da aka sata nan take, wanda ke karkashin jagorancin Mista Okoi Obno Obla, wanda ake zargi da cin hanci da rashawa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar da ya karbe ayyukan wannan kwamitin, sannan ya rusa shi, sannan ya tabbatar an kammala duk wasu bincike-bincike da aka fara ba tare da bata lokaci ba.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Umar Farouk Musa, daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5