Jami'an kiwon lafiya na tarayya, sun samar da wasu matakai na gaggawa da za su magance cututtukan huhu da sigari mai amfani da lantarki ke haifar wa.
A jiya Litinin, shugaban hukumar da ke kare yaduwar cututtuka ta CDC, Dakta Robert Redfield, ya ce ya ba da fifiko a gano abin da ke haifar da wannan yaduwar cuttutuka, da sigarin ke haifar wa wanda har yakan kai ga mutuwa.
Ya zuwa jiya Litinin, CDC tana kan binciken mutane 380, da aka tabbatar ko ake zargi da kamuwa da wasu cututtukan da ke da nasaba da cutar huhu ciki har da mutuwar mutum shida.
Masana harkokin kiwon lafiya, sun kasa fahimtar ainahin abin da ya faru, game da wata keɓaɓɓiyar alama da kuma sinadarin da ke kunshe a cikin sigarin, amma suna roƙon duk masu amfani da sigarin da su daina.
Ana tallata na’urorin da ce wa ba su kai tabar sigari illa ba. Masu tsara dokoki na gwamnati tarraya, sun gargadi babban kamfinin da ke kera sigari mai amfani da lantarki na JUUL, game da yin irin wannan ikirarin suna cewa ba a tabbatar da su ba.
Facebook Forum