ABUJA, NIGERIA - Da ya ke amsa tambayar manema labarai a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya bayan Sallar idin babbar Salla, Shugaba Buhari ya bayyana takaici kan yadda wasu miyagu kan kai hari kan jama’a haka kawai don mugun nufi.
Haka kuma shugaban ya bukaci jama’a su rika fallasa labarin maboyar miyagun ga jami’an tsaro don a kamasu a hukuntasu.
Da aka tambaye shi ko me zai cewa ‘yan Najeriya kasancewar wannan ita ce shekararsa ta karshe da zai yi idin babbar Sallah a matsayin shugaban kasa, Shugaban a takaice ya ce “su zauna lafiya” sai ya kama hanya ya bar inda ‘yan jaridar su ke.
A watan Fabrairun badi ne dai za a gudanar da babban zabe a Najeriya yayin da shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na karshe a ranar 29 ga watan Mayu na 2023.
Ziyarar shugaba Buhari Daura na zuwa ne biyo bayan harin da aka kai kan wata tawagar motocinsa da ke kan hanyar zuwa Daura a cikin makon nan.
Your browser doesn’t support HTML5