Najeriya: Buhari Ya Sauka a Najeriya

Dawowar Shugaba Mohammadu Buhari Daga Birnin London

A yau Asabar shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya sauka a birnin Abuja, bayan Kwashe sama da watanni uku yana jinya a birnin London dake Burtaniya.

Tun da safiyar yau Asabar ne kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya fitar da sanarwar dawowar Buhari, ya kuma kara da cewa zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya da safiyar ranar Litinin.

Tun a ranar 7 ga watan Mayu Buhari ya bar Najeriya domin neman magani kan cutar da har yanzu ba a bayyana ba, lamarin da ya sa wasu kungiyoyi suke kira da ya dawo ko kuma ya sauka a mulki.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ya je jinya a kasar ta Burtaniya domin neman magani.

A watan Janairu ya fara fita, inda ya kwashe kusan watanni biyu daga baya ya dawo a watan Maris, sannan ya sake komawa a farkon watan Mayu.

A dukkanin tafiye-tafiyen nasa, shugaba Buhari ya kan mika ragamar mulki ga mataimakinsa Prof. Yemi Osinbajo.

A farkon makon nan ne masu zanga zanga suka yi wani gangami a Abuja, babban birnin Najeriya dauke da kwalaye da aka rubuta “ka dawo ko ka yi murabus.”

A jihar Legas ma an yi makamanciyar wannan zanga zanga.

A ranar Talatar da ta gabata ne kuma, magoya bayansa suka yi artabu da masu zanga zangar neman ya dawo ko ya yi murabus a wata kasuwa da ke Abuja, kamar yadda kafafan yadan labaran Najeriya suka ruwaito.