Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya fada cikin wata sanarwa jiya cewa kudurorin hana kalamun batanci da na daukan hukumci a hannu zasu sami kulawar da ta kamata domin su zama dokoki cikin karamin lokaci.
Inji Sanata Saraki hakan nada nasaba da yadda kalamai da lafuza dake kara dumama yanayi ke ci gaba da yaduwa a kasar. Kudurorin biyu idan sun zama doka zasu taimaka wajen hana 'yan Najeriya daukan doka a hannunsu.
Biyo bayan furucin na Dr Saraki 'yan Najeriya sun soma bayyana ra'ayoyinsu akan kudurorin biyu.
Wani yace matukar za'a aiwatar da dokokin babu son kai ko yaudara zasu yi tasiri saboda haka suna goyon baya.
Shi ko Adamu Sa'idu cewa yayi abun da ya kamata 'yan majalisa su yiwa mutane ba shi su keyi ba. Idan mutum na da aikin yi ba zai yi tunanen yin wata barna ba. Yace rashin abun yi ke ba mutum zarafin tunanen aiwata abu mara kyau. Inji shi a fito da abun da zai ba mutane aikin yi domin su ma su tsaya da kafafuwansu .
Wadanda suka mayar da martani na fatan 'yan majalisa ba zasu yi anfani da dokar ba su ci zarafin talakawa idan sun zargesu da rashin yi masu aiki. Kada su rufe bakin talaka da dokar muddin suka ki yin abun da aka zabesu yi.
A kan daukar doka a hannu Sanata Masa'ud El-Jibril Doguwa yace talakawa da jami'an tsaro daga shekarar 1999 zuwa 2003 sun taka rawar gani wajen daukan doka a hannunsu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Facebook Forum