Buhari Ya Fasa Tafiya London Duba Lafiyarsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin dage tafiyar ba, amma ta ce nan gaba za a bayyana wata rana daban.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dage ziyarar da zai kai birnin London na Birtaniya don duba lafiyarsa.

Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Juma'a ce ta bayyana hakan.

Sai dai fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin dage tafiyar ba.

"Za a bayyana ranar da zai yi tafiyar a nan gaba." In ji Adesina.

A ranar Alhamis fadar shugaban kasar ta sanar da cewa Buharin zai tafi London a ranar Juma’a don sake ganin likita.

Buhari zai tafi birnin London na kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni 2021, don komawa ya sake bibiyar lafiyarsa.” Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta ce.

Karin bayani akan: London, Birtaniya, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A baya an tsara akan cewa shugaban zai dawo a mako na biyu cikin watan Yulin da ke tafe a cewar Adesina.

A watan Maris Buhari ya je kasar ta Birtaniya inda ya je duba lafiyarsa, ya kuma kwashe kusan mako biyu a can kafin ya koma gida.

Da tafiyar ta yi wu, da ta kasance ziyara ta biyu cikin kasa da wata uku da shugaban zai kai London don ganin likita.

A shekarun baya, shugaban na Najeriya ya kan je a duba lafiyarsa, illa a bara da bai je ba, saboda annobar COVID-19 da ta karade duniya, ta kuma sa aka rufe hanyoyin tafiye-tafiye.