Shugaban Najeriya ya danganta talauci da matsalolin tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta ga irin sace-sacen arziki da ake yi. Yana mai cewa dole ne kasashen Afirka a yanzu su dubi hanyoyin da zasu saka ido da kuma sikeli na auna mayan laifuka da sace-sacen dukiyoyi da arzikin Afirka, wanda ke haddasa matsalolin tsaro da rashin ci gaba ga al’umar Afirka baki ‘daya.
Kalaman shugaban Buhari na zuwa ne a lokacin bude wani babban taron jami’an leken asiri na kasa da kasa a birnin Abuja, wanda ya sami halartar jami’an kasashen Afirka. An gudanar da kasidu da bayanai dangane da irin hadin gwiwa da hadin kai da ake bukata ga kasashen Afirka domin dakile satar dukiyar Afirka.
Da yake yiwa Muryar Amurka Karin haske kan jawabin shugaba Buhari, mai baiwa shugaban shawara ta fuskar labaru Mallam Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya dogara ne akan irin kididdigar da ake fitarwa kan yadda ake kwashe dukiyoyin ‘yan Afirka ana kaiwa wasu kasashe.
Ya ci gaba da cewa yayin da ake samun rahotannin ci gaba a sauran kasashen duniya, kasashen Afirka baya a ke komawa domin ana sace kudaden da suka kai Dala biliyan biyar.