Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce “an rasa rayuka da dama cikin makonnin da suka gabata an zanga zangar da aka yi, ba tare da ya ambaci masu zanga zangar da ‘yan sanda suka kashe ba, inda ya yi kira da a kawo karshen boren.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya yi da tsoffin shugabannin kasar a ranar Juma’a inda suka tattauna yadda za a shawo kan wannan tarzoma wacce Najeriyar ta jima ba ta ga irinta ba cikin shekarun da suka gabata.
A cewarsa “cikin wannan tashin hankali da ya faru, an rasa rayuka da dama an kuma barnata dukiyoyin gwamnati da na jama’a…. amma duk da haka ba a daina rikicin ba,” yana mai cewa, "jami’an tsaron sun iya bakin kokarinsu wajen ganin ba su fusata ba yayin da ake wannan rikici.”
Ya kuma kara da cewa, “gwamnati ba za ta nade hannu tana kallon bata-bari suna cin karensu ba babbaka ba.”
Sai dai shugaban na Najeriya bai fadi adadin mutanen da suk mutu ba, amma bayan taron, ya fada a wata sanarwa da ya fitar cewa, fararen hula 51 da ‘yan sanda 11 da sojoji bakwai ne suka mutu a lokacin wannan zanga zanga.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga hukumomin Najeriya da “kada su yi amfani da karfin tuwo wajen tunkarar masu zanga zangar” yana mai cewa ya samu tabbaci daga shugaba Muhammadu Buhari cewa, ba za a yi hakan ba.
A ranar Alhamis Amurka ta yi Allah wadai da matakin da ‘yan sanda suka dauka akan masu zanga zangar a Legas, inda Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya nemi da a gudanar da bincike.
Najeriya ta shiga rudanin zanga zanga ne a lokacin da ake ta kiraye-kirayen a rusa rundunar SARS da aka kafa ta don yaki da 'yan fashi.
Hukumomi sun rusa rundunar amma duk da haka zanga zangar ta dore a wasu sassan Najeriyar.