Wata sanarwa da mai baiwa shugaba Buhari shawara kan hulda da jama’a da ‘yan jarida, Femi Adesina, ya ce mai baiwa Buhari shawara kan harkar tsaro, Major-General Babagana Monguno mai ritaya, da manyan jami’ai a ma’aikatun tsaro da kudade da noma da harkokin wajen Najeriya, na daga cikin wadanda suka rufawa shugaba Buhari baya a wannan ziyara.
A cewar sanarwar ta Adesina, irin tawagar da Buhari ya tafi da ita, alama ce da ke nuna cewa tattaunawa shugabanin biyu za ta ta’allaka ne kan yadda za a karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka hada da tsaro da huldar kasuwanci da kuma saka hannayen jari.
Ana sa ran da yammacin yau ne Hollande zai gana da Buhari a fadarsa ta Alysee da ke Paris inda har ila yau ake kuma tunanin shugaban na Najeriya zai gana da ministan tsaron Faransa, Jean-Yves Le Drian da ministan kudi Michel Sapin da sauran manyan jami’an gwamnatin Faransa.
A ranar Laraba mai zuwa ake sa ran Buhari zai dawo Najeriya bayan kammala wannan ziyara.
Ibrahim Ka'almasi Garba ya tambayi Malam Aminu Sule mai fashin baki a harkar diplomasiya kan tasirin wannan ziyara ga kuma yadda hirarsu ta kaya:
Your browser doesn’t support HTML5