Wannan sako yazo ne ta bakin mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu, a hira da yayi da Sashen Hausa na Muryar Amurka.
“Su jami’ai na tsaro da suke shugabancin wannan yaki da akeyi, suna sanar da gwamnati cewa.. ka san yanzu gwamnati ta tsananta ita kanta nata gudunmuwar. An tura karin sojoji a wadannan bangarori, an tura makamai wadanda da babu su, an kuma tura jirage masu shawagi dare da rana. Duk inda suka ga gungun wadannan masu tayar da kayar baya, ko a dauki hotonsu a sanar, ko a kai musu hari ma in ta kama” a cewar Garba.
Ya cigaba da cewa “abunda suke nuna wa gwamnati shine an tarwatsa su daga sansanoninsu. Sun bazama, sun nufi kasa daban-daban. Saboda haka, abunda suke kamar abunda ake cewa ‘rungume-ni-ka-fadi’ ne. Duk inda suka ga wata dama wadanda zasu yi barna, zasu yi. Shiyasa gwamnati take bada shawara ga jama’a cewa ayi hattara. A sa ido a ringa kula.”
To ko wani sako shugaban yake da shi ga jama’ar Najeriya wadanda wannan lamari ya saka a cikin zaman dar-dar?
Mallam Garba yace “(Buhari) yana cikin bakin ciki da damuwa a halin da suka samu kansu a ciki, yana jajanta musu, da ‘yan uwa da duk wadanda suka rasa wasu nasu, da daukacin ‘yan Najeriya baki daya. Saboda rashin nan gaba daya ya shafe mu. Kuma yana jaddada cewa idan gwamnatinsa ta kafu, yana da niyyar cewa wannan hali da mutane suka samu kansu a ciki in Allah Ya yarda za’a taimaka a yi maganinsa. Sannan a sake gina tattalin arziki da harkar rayuwa ta jama’a, a duk wannan bangarori na Najeriya da fitina ta dame su.”
Ya zuwa yanzu an share kusan shekaru 6 ana fama da rigingimun Boko Haram da suka tarwasta rayuwa da zamantakewar al-ummomi da yawa a arewacin Najeriya. Shugaba Buhari wanda aka zaba a matsayin sabon shugaba a watan Mayun wannan shekara ya dauki alwashin kawo karshen matsalar.
Your browser doesn’t support HTML5