BORNO: Kungiyar Lauyoyi Ta Zargi Sojoji da Cin Zarafin Jama'a

Sojojin Najeriya a Maiduguri

A shirin mulkin dimokradiya sojoji basu da hurumin kafa dokar hana fita a koina a Maiduguri-inji kungiyar layoyin jihar Borno dake Maiduguri.

Abdulwasiu Alhaji Alfa shugaban kungiyar lauyoyin Maiduguri shi ya bayyana makasudin kiran taron manema labarai da kungiyar ta yi.

Alfa yace sun lura mutanen Maiduguri masu hakuri ne saboda haka sojoji sun samu zarafi suna cin mutuncinsu. Yace idan rikici ya faru a jiha babu inda doka tace a hana fita fiye da awa 24. Yace mutane suna da 'yancin su fita. Amma ranar Laraba an hana fita na tsawon awa 24. Mutane sun fito ranar Juma'a da safe aka sake komar dasu gidajensu.

Yace bayan hakan ya faru sun koma su duba takardun su na shari'a da na dokokin Najeriya gaba daya. Sun gano cewa soja ma bashi da hurumin kafa dokar ta baci. A cikin mulkin dimokradiya soja bashi da ikon yace mutane ba zasu fita ba. Karya ne. Soja bashi da iko kuma bashi da hurumin yin hakan.

Dangane da wai sojoji sun dauki matakin ne domin kare jama'a Abdulwasiu Alfa yace kamata ya yi mutane su fito su yi walwala domin sun san sojoji na nan suna karesu ba wai su hana mutane fita ba. Ba wai zasu kori mutane su shiga gidajensu ba amma idan ana kawo hari su sojojin gudu suke yi.

Shugaban lauyoyin yace babu wanda yake da hurumin daukewa mutane zirga-zirga. Yace daga shugaban rundunar sojoji na kasa har kasa zasu gurfanar dasu gaba kotu domin basu fi karfin kotu ba. Zasu tambayi kotu ta fada masu a shirin dimokradiya inda akwai gwamna sojoji zasu iya yin dokar hana zirga zirga.

Dokar hana fita da sojojin suka kafa wata hanya ce da suke anfani da ita suna samun kudi. Yace lokacin da ake da dokar hana fita da zara lokacin dokar ya yi sai sojoji su dinga karbar kudi a hannun wadanda dokar ta samu a waje. Su kan karbi nera dari biyu har zuwa dubu daya.

Abun dake faruwa a Maiduguri tamkar akwai gwamnoni biyu ne. Daya a gidan gwamnati daya kuma a barikin sojoji. Gwamna ya kamata ya kafa dokar hana fita ba soja ba.Idan soja na so ya kafa doka to ya tube kakinsa ya tsaya zabe. Idan an zabeshi to sai ya kafa doka.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

BORNO: Kungiyar Lauyoyin Borno Ta Zargi Sojoji da Cin Zarafin Jama'a - 4' 16"