Wani harin bam da aka kai a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya halaka akalla mutane bakwai.
Harin ya faru ne a kusa da wata tashar mota a Damaturu, babban birnin jahar.
Waklin Muryar Amuraka a yankin ya ce wata mata ce 'yar kunar bakin waketa ta da bam din a lokacin da ake binciken ta a wata tashar mota.
Baya ga wadanda suka mutu akwai wasu kuma da dama da suka samu raunuka in ji wakilin Muryar Amurka.
Yobe ta kasance daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar hare-haren kungiyar Boko Haram, domin ko a watan Janairun wannan shekara an kai wasu hare-haren bama-bamai a wata kasuwa.
Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya, ya kasance tushen ‘yan kungiyar Boko Haram masu ta da kayar baya, inda dakarun kasar ke kokarin dakile ayyukan ‘yan kungiyar.
Ga karin bayani a hirar wakilinmu Haruna Dauda da Aliyu Mustaphan Sokoto: