Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tura Fa Ta Kai Bango -inji Captin Abdullahi


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Idan aka yi la'akari da yadda aka rufe dukkan iyakokin kasashe makwabta wato Chadi da Nijar da Kamaru, ga sojojin kasashen girke dole ne su fuskanci matsalar wurin boyo.

Dangane da harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a ranar larabar da ta gabata a garin Maiduri wanda yayi sanadiyyar raunata sojoji guda biyu da kuma jama’a da dama waddanda har yanzu ba’a san adadin mutanen da suka rasa rayukan su ba, Mahmud Lalo yayi hira da wani Jami’in sojin Najeriya mai ritaya Captain Abdullahi Bakoji Adamu inda yace;

“abin da ke faruwa yanzu haka shine tura ce ta kai bango a sakamakon rufe iyakokin Kamaru da Chadi da Nijar da akayi, ‘yan kungiyar ta Boko Haran sun rasa inda za su shiga kamar yadda suke yi da, wato idan an kora su, yanzu akwai jami’an tsaron kasar girke akan iyakokin kasashen”.

Yayi Karin bayanin cewa akwai sauran ‘yan kungiyar a cikin garuruwa da dama harda inda ba’a yi tsammani ba kuma ganin cewa an tura su har bango, dalili Kenan yasa suke kokarin kutsa wa cikin wasu garuruwa domin samun wurin buya, kuma kullum kama su akeyi ba dare ba rana.

Dangane da kalaman gwammantin Najeriya a kwanakin baya na cewar zata kawo karshen wannan matsalar kafin babban zaben kasar da aka gudanar, tsohon jami’in yayi Karin bayanin cewar “ni nasan dama duk alkawarin da suka yi nasan Najeriya bata shirya ba, ko da alokacin da abin yayi tsanani sojojin Najeriya na iya shawo kan wannan matsalar sai dai kawai anga dama ne”.


Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG