BORNO: Kungiyar Boko Haram Ta Hallaka Mutane 46

Wadanda suka samu rauni kwance a asibiti

Ranar Talata da misalin karfe takwas da rabi na dare ne wasu mahara da ake kyautata zaton 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka afkawa kyauyen Musaram cikin karamar hukumar Mongunu ta jihar Borno.

A wannan harin maharan sun harbe mutane 46 har lahira kana suka ji ma wasu shida.

Mayakan Boko Haram suna cigaba da zafafa kai hare-hare musamman na kunar bakin wake a kauyuka da ma wasu garuruwa dake kusa da birnin Maiduguri tun lokacin da sabuwar gwamnatin Buhari ta bullo da shirin kawar da kungiyar

Abun dake faruwa na daurewa mutane kai ganin cewa rundunar sojojin Najeria ta kaura zuwa Maiduguri domin karfafa yaki da fafatawa da 'yan ta'adan Boko Haram. To saidai duk da wannan sabon tsarin hare-haren sai karuwa suke yi yayinda kuma 'ya'yan kungiyar na sulalewa salin-alun bayan sun aikata barna.

Mutane na zaton hare-haren na faruwa ne ganin irin nasarar da jami'an tsaro ke samu akan kungiyar dalili ke nan suke kai hari kan maiuwa da wabi.

Daya daga cikin mutanen garin Mongunu ya kara haske akan abun da ya faru. Yace wadanda aka raunata suna asibitin Umaru Shehu dake cikin garin Maiduguri.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu

Your browser doesn’t support HTML5

Borno: Kungiyar Boko Haram Ta Hallaka Mutane 46 - 1' 49"


.