Borno: Harin Da ‘Yan Boko Haram Suka Kai Maiduguri

Harin Da Boko Haram Ta Kai Unguwar Jiddari-Pollo.

Biyo bayan harin ta’addanci da aka kai unguwar Jiddari-Polo a yammacin Laraba, hankalin mutanen unguwar ya tashi inda har suka arce suka bar gidajensu.

Tun da misslin karfe biyar na maraicen jiya ne dai aka rinka jin karar harbe-harbe, wanda ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi kokarin kutsawa cikin garin Maiduguri, inda daga bisani rundunar sojan Najeriya ta taka musu birki.

An kwashe kusan sa’o’i uku ana ta jin ‘karan harbe-harbe tsakanin rudunar sojan ‘kasa da maharani, wanda yasa mazauna unguwar hada kayansu da ficewa daga unguwar, wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya zanta da wasu mutanen dake gudun hijira daga unguwar Jiddari-Polo zuwa wasu unguwannin, inda suka shaida masa cewa har zuwa lokacin da suka baro gidajensu suna ta jin karan harbe-harbe.

Harin Da Boko Haram Ta Kai Unguwar Jiddari-Pollo.

A wani rahotan na daba kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wanda kuma ya kasance shugaban gwamnonin Arewa 19, ya kushewa kungiyoyin matasan nan na Arewa da sukace ya kamata ‘yan kabilar Igbo dake a arewacin kasar su fice daga yankin, wanda gwamnan yace bai dace ba, kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ya baiwa duk wani kabila ko kuma wanne addini ya zauna a duk inda yake so.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Borno: Harin Da ‘Yan Boko Haram Suka Kai Maiduguri - 3'29"