Borno: Gwamnatin Najeriya Ta Nemi Karin Taimakon Amurka Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa

  • VOA Hausa

Kashim Shettima da Antonio Gutteres

Yayin ganawan sun tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi tsaro a yankin Afirka ta yamma da harkar bada agaji da kuma rawar da Najeriya ke takawa a fannin bada gudunmowa tsakanin kasa da kasa.

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya gana da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a shelkwatar majalisar dake birnin New York.

Yayin ganawan sun tattaunawa a kan batutuwan da suka shafi tsaro a yankin Afirka ta yamma da harkar bada agaji da kuma rawar da Najeriya ke takawa a fannin bada gudunmowa tsakanin kasa da kasa.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron kolin Majalisar Dinkin Duniya karo na 79, ya samu tarba zuwa ginin majalisar daga Mataimakiyar Babban Sakatarenta, Amina Muhammad, inda suka yi wata kwarya-kwaryar ganawa biyo bayan tattaunawarsa da babban sakataren.

A yayin ganawar, mataimakin shugaban kasa Shettima ya jaddada tsananin bukatar samar da agaji domin shawo kan matsalar sauyin yanayi sannan ya yi jan hankali a kan bukatar bada tallafi domin magance barnar da mazauna jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya suka fuskanta a baya-bayn nan.

A nasa bangaren, babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, Antonio Guterres, ya bayyana ta’azziyarsa game da asarar rayukan da aka samu a Najeriya a baya-bayn nan, inda ya sha alwashin samarda karin tallafi daga majalisar.