Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayara baya a arewa maso gabashin Najeriya, ta kai wasu hare-hare a kauyan karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa.
A cewar wani mazaunin daya daga cikin kauyukan, maharan sun farma kauyen Kaya ne da ke da tazarar kilomita daya daga garin Gulak, hedikwatar karamar hukumar Madagalin.
Shaidu sun ce sun kuma sace mutane uku da mota, sannan sun karyawa wata dattijuwa kafa.
Bayan da marahan suka bar kauyukan ne, jami’an tsaro suka shiga yankin da aka kai hari suna harbe-harbe a cewar wani mazaunin kauyen.
Ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaro ba su yi karin haske game da wannan sabon hari da aka kai cikin daren jiya Alhamis ba.
Amma kuma shugaban karamar hukumar ta Madagali Hon.Yusuf Muhammad ya tabbatar da faruwan lamarin, inda har ya yabawa yan sakai na maharba da suka tarwatsa harin da aka soma kaiwa a Milbu.
Shi ma da yake karin haske, dan Majalisar wakilai da ke wakiltar yankin, Mr. Adamu Kamale, ya koka da harin da ake kai wa cikin kwanakin nan, tare da neman gwamnatin tarayya ta aika sojoji zuwa yankin kasancewar ba su da nisa da dajin Sambisa da ya kasance tungar mayakan na Boko Haram.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz:
Your browser doesn’t support HTML5